Kaduna: ‘Yan Bindiga Da Dama Sun Mutu A Rikicin Cikin Gida

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Hukumomi a jihar sun ce wasu mambobin kungiyoyin ‘yan bindiga da ke gaba da juna su tara sun rasa rayukansu sanadin musayar wuta a yankin ?aramar hukumar Giwa.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce rikicin ya faru ne a wani ?auye da ke ?aramar hukumar ta Giwa.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ya ce majiyoyin tsaro sun ba da rahoton cewa wani shahararren dan fashi da aka fi sani da ‘Godon Mota’ da yaransa sun abka wa kauyen Garke a ranar Larabar da ta gabata inda suka yi arangama da wata kungiyar’ yan fashi da makami.

Ya ce lamarin da ya yi sanadin ‘yan bindiga tara nan take, galibin su manyan kwamandoji ne.

“Har yanzu ba a san musabbabin tashin hankalin ba amma an ce ya danganci rashin jituwa kan raba kudaden fansa, wanda a lokacin daya daga cikin kungiyoyin ya ji cewa an yaudare shi,” in ji shi.

Ya kara da cewa: “Mukaddashin Gwamna Dakta Hadiza Balarabe ta yi maraba da rahoton, sannan ta bukaci hukumomin tsaro da su ci gaba da matsa lamba kan cafke masu aikata laifuka a yankin baki daya.”

Ba wannan ne karon farko da kungiyoyin ‘yan fashin daji suke samun sabani a tsakaninsu ba lamarin da kan kai su ga hatsaniya.

Ko a watan Mayun da ya gabata rikici tsakanin ‘yan bindigar da ke gaba da juna ya yi sanadin mutuwar Auwalu Daudawa, kasurgumin dan fashin dajin nan da ke da hannu wajen sace daliban sakandaren Kankara.

Kaduna na cikin jihohin da ‘yan fashi a cikin daji ke tasiri inda su ke garkuwa da mutane da dama domin karbar kudin fansa.

Har yanzu akwai mutane da dama da suke garkuwa da su da suka ha?a da daliban makarantar sakandire ta Bethel Baptist da suka yi awon gaba da su a ?aramar hukumar Chikun

Related posts

Leave a Comment