Kaduna: ‘Yan Ƙato Da Gora Sun Hallaka Matashi

Lamarin ya faru ne a ranar laraba inda marigayin mai kimanin shekaru 25 ya je wani gida anan Layin All saint dake sabon garin tudun wada domin gyaran wutar lantarki, shigarsa keda wuya matar gidan tace ba nan gidan zaiyi gyaran wuta ba, yadai kira Wanda ya turoshi a waya. Ya fita kofar gidan sai wani matashi dake zama a gidan yace shi bai yarda da take taken sa ba domin yana ganin kamar barawo ne.

Nan kuwa ya mikawa jami’an kato da goro dake wannan yankin Mansir akan su tuhume shi. Bayan ya dawo da daddare jikin sa duk rauni, sai yayan sa yaje gidan matar inda ta bayyanawa yayan cewa Mansir bai daukar masu komai ba, kawai gyara yazo tace mai ba gidan bane amman ita bata cewa kowa ya mata sata ba. Yayan ya kammala bincike kamar yadda ya shaidawa wakilin jaridar muryar Yanci cewa yana son kai karar su wurin hukumar yan sanda a safiyar yau jumma’a sai kuma Allah ya dauki ransa da asubahin yau.

Mahaifiyar Mansir Kabir ta shaidawa wakilin Jaridar Muryar Yanci cewa ” ita tasan gidan matar da yaronta yaje har akai masa raunin da yai sanadiyyar mutuwar sa, Sannan tasan jami’an kato da Goran da suka kashe mata yaro. Dan haka bawai zargi ake yi ba, Dan haka tana kira ga gwamnatin jihar Kaduna ta dauki mataki tun kamin tabar yan uwansa su dauki doka a hannu.

Shima a nasa jawabin kawun Mansir yayi kira ga kungiyoyin kare hakkin dan Adam da gwamnatin jihar Kaduna akan sudauki mataki domin saida ya tsawatawa abokan marigayin akan karsu dauki mataki har sai anjira hukumomin da lamarin ya rataya a wuyan su.

Wakilin jaridar Muryar Yanci ya ziyarci ofishin jami’an KADVS domin jin ta bakin su, amman sun shaida mana cewa tabbas an kawo Mansir wurin su ana zargin sa da sata, kuma lokacin da aka kawo shi wurin sun ganshi a buge shiyasa suka sallame shi kawai. Kila a hanyar sa ta komawa gida ne ya hadu da wasu suka dake shi. Sai wakilin mu ya tanbayesu meyasa basu ajiye sa a nan ba har sai ya dawo hayyacin sa kamin suyi binciken su? Sai suka ce wannan tanbayar shugaban su ne Alh Zailani zamu tanbaya domin shine jagoran su. Mun kira Zailani harya zuwa lokacin da muke rubuta wannan ruhoto amman wayar sa a kashe.

Labarai Makamanta

Leave a Reply