Kaduna: Uba Sani Ya Zabi Hadiza Balarabe Mataimakiya

Rahotanni daga jihar Kaduna na bayyana cewar ?an takarar gwamnan Kaduna a ?ar?ashin Jam’iyyar APC Sanata Uba Sani ya ?auki mataimakiyar gwamnan jihar ta yanzu wato Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin mataimakiya a takarar za?en 2023.

Sanata Sani ne ya bayyana haka a wani sa?o da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya ce ya yi wannan za?e ne bayan ya tuntu?i masu ruwa da tsaki na Jihar Kaduna.

Sanata Uba Sani ya bayyana cewa Hadiza ta bayar da gudunmawa a gwamnatin Nasir El-Rufai wajen gudanar da ayyukan ababen more rayuwa da kuma gina rayuwar al’umma.

Uba Sani na Jam’iyyar APC zai kara ne da Isah Ashiru Kudan na Jam’iyyar PDP a za?en 2023 da ke tafe.

Related posts

Leave a Comment