Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Jami’an tsaro sun harbe kwamandojin ‘yan bindiga 10 a Kwanan Bataru, wajen Fatika da ke karkashin karamar hukumar Giwa a jihar.
Sannan har maboyar ‘yan bindigar ma ba ta tsira ba, sai da jami’an tsaron su ka banka ma ta wuta, suka fatattaki sauran ragowar ‘yan Bindigar da suka saura.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata takarda sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
A cewar sa, jami’an tsaron sun tseratar da wani Alhaji Abubakar Usman daga hannun ‘yan bindiga a yankin. Aruwan ya kara da bayyana yadda wasu ‘yan bindiga su ka sha dakyar inda su ka tsere tare da manta babura, tociloli da layun su. Akwai wani wuri da su ke zama, shi ma jami’an tsaro sun yi wa wurin kurmus da wuta..