Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Kaduna: Shugaban ?ungiyar Masu Sayar Da Motoci Ya Sha Alwashin Kai Kungiyar Gaba

FB IMG 1718177211354

Shugaban ?ungiyar masu sayar da motoci ta ?asa reshen Jihar Kaduna Alhaji Aminu Ibrahim ?an ?a?alo ya bayyana cewar babban kudurin da ya sa a gaba shine zamanantar da tsarin ?ungiyar zuwa ga mataki na cigaba.

Aminu ?an ?a?alo ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da da ya yi da manema labarai kan kudurorin Shugabancin sa a sakatariyar ?ungiyar dake garin Kaduna.

?an ?akalo ya ?ara da cewar ?ungiyar tasu tana cikin wani yanayi na rashin wayewar zamani a tsawon lokaci kusan shekaru 40, inda ya sha alwashin ?ora ‘ya’yan kungiyar a tsarin wayewar zamani ta hanyar saye da sayar da motoci domin dacewa da muradun karni.

Aminu ?an ?a?alo ya kuma yi kira ga kafatanin ‘ya’yan kungiyar da su rungumi akidar ha?in kai da juna domin babu wata kungiya da za ta cigaba a rayuwa matukar babu hadin kai a tsakanin su.

Aminu ?an ?a?alo ya kuma yaba salon jagorancin Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani na raya Jihar Kaduna, inda ya bayyana goyon bayan ?ungiyar tasu wajen kai Jihar Tudun mun tsira.

Exit mobile version