Shugaban Ƙungiyar masu sayar da motoci ta ƙasa reshen Jihar Kaduna Alhaji Aminu Ibrahim Ɗan Ƙaƙalo ya bayyana cewar babban kudurin da ya sa a gaba shine zamanantar da tsarin Ƙungiyar zuwa ga mataki na cigaba.
Aminu Ɗan Ƙaƙalo ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da da ya yi da manema labarai kan kudurorin Shugabancin sa a sakatariyar Ƙungiyar dake garin Kaduna.
Ɗan Ƙakalo ya ƙara da cewar Ƙungiyar tasu tana cikin wani yanayi na rashin wayewar zamani a tsawon lokaci kusan shekaru 40, inda ya sha alwashin ɗora ‘ya’yan kungiyar a tsarin wayewar zamani ta hanyar saye da sayar da motoci domin dacewa da muradun karni.
Aminu Ɗan Ƙaƙalo ya kuma yi kira ga kafatanin ‘ya’yan kungiyar da su rungumi akidar haɗin kai da juna domin babu wata kungiya da za ta cigaba a rayuwa matukar babu hadin kai a tsakanin su.
Aminu Ɗan Ƙaƙalo ya kuma yaba salon jagorancin Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani na raya Jihar Kaduna, inda ya bayyana goyon bayan Ƙungiyar tasu wajen kai Jihar Tudun mun tsira.