Kaduna: Sace ‘Yan Jarida Ba Abin Lamunta Bane – Kungiyar Matasan Arewa

images (71)

Kungiyar cigaban Matasan Arewa (AYCF) ta yi tir gami da Allah wadai da yin garkuwa da wasu ‘yan jarida biyu da iyalansu da ‘yan Ta’adda su kayi a Kaduna.

A cikin wata takardar sanarwa da shugaban kungiyar na ƙasa Alhaji Yerima Shettima ya fitar, ya bayyana sace ‘yan Jaridar a matsayin tsagwaron rashin imani sannan ya yi kiran sakin su cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.

Shettima ya ƙara da cewar labari ne mai tayar da hankali sace Alhaji Abdulghaffar Alabelewa na jaridar The Nation da matarsa da ‘yayansa biyu, a gefe guda kuma da sace Alhaji Abdulraheem Abdul na jaridar Blueprint.

Shugaban kungiyar ya yi kira da babbar murya ga hukumomin gwamnati da na tsaro da cewar su yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an ceto ‘yan Jaridan daga hannun miyagun.

Shettima ya kuma yi kira ga dukkanin al’umma da su sanya ‘yan jaridar cikin addu’o’i domin samun kubuta daga halin da suke ciki.

“Bai kamata ‘yan Jarida su zama abin farauta da za a rinƙa garkuwa dasu ba, duba da irin tasirin da suke dashi a cikin al’umma, na ciyar da ƙasa gaba”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply