A yayin da ‘yan kasuwa ke hada-hadar cin kasuwar bikin kirsimeti, gwamnatin jihar Kaduna ta yi dirar mikiya a babbar kasuwar Kakuri da ke cikin Karamar Hukumar Kaduna Ta Kudu a jihar , inda ta fara rushe daukacin shagunan ?da ke cikin kasuwar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wata ‘yar kasuwa.
‘Yar kasuwar mai suna madam Merry, ta mutu ne yayin da ta Hango wata katuwar Katafila tana ruguza Shagonta, lamarin da sanya mata bugun zuciya wanda nan take ta ce ga garinku nan.
Gwamnatin ta karkashin hukumar tsara birane na jihar (KASUPDA) ?ta dauki matakan rushe kasuwar ne domin sake Gina kasuwar ta zama irin ta zamani kamar yadda tace.
A ziyarar da wakilinmu ya Kai kasuwar ya tarar da ‘yan kasuwar suna zaman jimamin Rasa daya daga cikin su, a bangare guda kuma suna jimamin rusa daukacin shagunan.
Sai dai a yayin da ake rushe kasuwar matasa bata gari suma sun kukufa wajen balle shagunan ‘yan kasuwan, lamarin da ya kara tada hankulan ‘yan kasuwan.
‘Yan kasuwar sunce gwamnatin jihar ta basu wa’adin mako daya ne kacal wanda kuma bai isa su kwashe kayansu ba inda sukayi Allah wadai da matakin Rusau a kasuwar.
‘Yan kasuwar da suka zanta da wakilinmu, Sun nuna rashin gamsuwarsu dangane da matakin da gwamnatin ta dauka a yayin da suke cin kasuwar Kirsimeti, inda sukayi Allahwadai da matakin.
Malam Abubakar Mila, Zan kasuwa a kasuwar na kakuri, yace ” bamuji dadin wannan abu da gwamnati tayi ba saboda ai muna da ‘yancin a bamu wa’adi mai tsawo kuma a Sama mana wani wurin da zamu koma amma da rana tsaka kawai a fado mana kasuwa a fara rushe mana shaguna, gaskiya wannan rashin tausayin yayi yawa” inji Mila.
Yace bayan ‘yan rundunar jami’an sa kai JTF sun kawo musu dauki da basu San irin asarar da zasu tafka ba, Biyo bayan yadda barayi suka yiwa kasuwar dirar mikiya suna balle shaguna suna kwashe kayansu yana mai cewa suna kira ga gwamnatin jihar data tausaya musu ta samar musu da wani wurin da zasu koma domin ci gaba da harkar kasuwancinsu.
Babbar kasuwar Kakuri, kasuwace wacce musulmi da kirista suke gudanar da hada-hadar kasuwancinsu cikin lumana musamman ma a irin wannan lokacin da ake shirin gudanar da bikin kirsimeti da sabuwar shekara wanda kasuwar take cika ainun.
Wakilinmu ya ziyarci hukumar ta KASUPDA domin ta bakinsu, inda ya tarar da shugaban hukumar wanda shine ya jagoranci rushe kasuwar bai tarar dashi ba amma wani babban jami’i a hukumar ya shaidawa wakilinmu cewa gwamnati ta yanke shawarar rushe kasuwar ne domin mayar da ita ta zamani.