Kaduna: Mr. LA Ya ?alubalanci Gwamnati Da Ceto ?alibai

Honorabul Lawal Adamu Usman Mr LA ya kalubalanci gwamnati akan ta tabbatar ta ceto yaran da yan bindiga suka sace a kwalejin gandun daji dake kaduna.

Mr LA ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da menema labarai a ofishinsa dake Kaduna. In da yace ”Ya kamata gwamnati tai iya bakin kokarinta wurin kare aukuwar hakan a nan gaba duk da a wani bangaren dole ne mu kara jinjinawa jami’an tsaron mu ganin yadda sukayi kokari sosai wurin ceto dalibai 180 a ranar da abin ya faru.

Daga karshe Mr LA ya shawarci gwamnonin yankin arewa dasu hade kansu wuri daya, su ajiye duk wani banbanci dake tsakanin su, su zauna su fitar da hanyoyin da zasu kawo katshen matsalaolin dake addabar arewa. Domin a yanzu sune keda alhakin yin hakan kuma ya zama wajibi su ceto arewa daga halin da take ciki.

Dan wallahi idan aka cigaba da kaiwa makarantun mu na arewa hari kamar yadda akeyi a halin yanzu, za a kai wani lokacin da yaran ma zasu dena zuwa makarantar gaba daya kuma daman an bar yankin mu na arewa a baya musamman a fannin ilimi.

Related posts

Leave a Comment