Kaduna: Matar Zakzaky Ta Warke Daga CORONA

Lauya mai kare Uwargidan Shugaban ‘Yan Shi’ar Najeriya Zeenatu Zakzaky Barista H.G. Magasahi a madadin Femi Falana ne ya nemi babbar kotun Kaduna ta soke umarnin da ta bada a baya na akai Zeenatu asibiti domin kula da ita sakamakon harbuwar da cutar CORONA.

Bisa ga haka, kotun ta janye umarnin bayan lauya, H.G. Magashi daga ofishin Falana ya furta wa kotun da baki cewa Zeenatu ta warke daga cutar wadda aka shelanta cewa ta kamu da ita a kwanakin baya.

A cewar Mai Shari’a Gideon Kurada, “sakamakon bukatar da H.G. Magashi ya shigar a madadin Femi Falana SAN, masu kare wanda ake kara na farko na biyu Edwin Inegedu Esq suna bukatar kotun ta yi watsi da batun kai wacce ake kara ta biyu zuwa asibiti.

“Lamarin ya canja ne saboda wacce ake kara ta biyu ta warke kuma hukumar kula da gidajen yarin na Kaduna ta bata damar ganin likitocinta.

Don haka tana son janye bukatar da ta shigar a ranar 26 ga watan Janairun 2021,” in ji shi.

Idan ba a manta a ranar 26 ga watan Janairu, Mai shari’a Kurada ya umurci a saki Matar Zakzaky bayan lauyanta Femi Falana ya gabatarwa kotu rahoton likita sannan ya bukaci kotun ta sake ta domin a yi mata maganin COVID 19 kamar yadda NCDC ta tanada.

Related posts

Leave a Comment