Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa yana sauraron masu zaben sarki a masarautar Zazzau su gabatar masa da shawarwarinsu kan sabon sarkin da za’a nada.
El Rufa’i ya bayyana cewa lallai ya lura mutane da dama sun zuba ido kan wanda za’a zaba, kuma saboda haka yayi addu’a Allah ya baiwa masu zaben Sarki hikiman zaban Sarki mai irin dabi’un marigayi Alhaji Shehu Idris.
Mai magana da yawun El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Laraba. Yace: “Tun da an kammala kwanakin makoki, gwamnatin jihar Kaduna na sauraro cikin ‘yan kwanaki masu zuwa shawararin masu zaben sarki a masarautar Zazzau game da sabon sarki.”
“Al’umma su saurari sanarwar gwamnati kuma suyi watsi da jita-jita, kiyase-kiyase da labaran karya.”
“Dubi ga yadda yada ra’ayoyin mutane ya janyu kan lamarin wanda zai hau kujerar sauratar Zazzau, El-Rufa’i ya yi addu’a Allah ya baiwa masu zaben sarkin hikima.”
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmed El Rufai, ya bayyana cewa tun ranar da marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya rasu, ba ya iya bacci sai ya sha magani saboda tsananin baƙin ciki.
Gwamnan ya bayyana hakan ne wajen taron addu’ar sadakar uku na Marigayin da ya gudana ranar Laraba, 23 ga Satumba, 2020,
Manyan mutane da dama sun halarci taron addu’ar. Daga cikinsu akwai tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo; Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru; Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong.