Mahaifin ?aya daga cikin ?aliban makarantar koyar da dabarun noma da gandun daji FCFM Afaka 39 da yan bindigan suka sace a jihar Kaduna, Ibrahim Shamaki, ya mutu sakamakon bugun zuciya.
An ruwaito cewa Alhaji Ibrahim Shamaki mahaifi ne ga Fatima Shamaki, daya daga cikin dalibai matan da suka bayyana a bidiyon da yan bindigan suka saki.
A cewar majiya daga iyalan mamacin, Ibrahim Shamaki ya mutu sakamakon bugun zuciya bayan rashin lafiyan da ya fada sakamakon samun labarin sace diyarsa.
Ya mutu da yammacin ranar Juma’a yayinda yan’uwansa ke kokarin kai shi asibiti.
Labarin mutuwar Alhaji Ibrahim na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta zauna da wakilan iyayen daliban a gidan gwamnatin jihar, makwanni biyu kenan da sace daliban.
Kun ji cewa malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Gumi, ya yi magana game da daliban makarantar ta Kaduna da aka yi garkuwa da su.
Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce umarnin da aka ba jami’an tsaro na harbe duk wanda su ka gani ya na dauke da bindigar AK-47 ya sa aka gaza ceto daliban.
Da yake magana da Daily Trust, malamin ya ce ya hadu da wasu ‘yan bindiga da su ka taimaka masa har ya gano gungun wadanda su ka sace wadannan dalibai.