Kungiyar Lauyoyi Musulamai a jihar Kaduna MULAN, ta sanar da janyewa daga taron gangamin Lauyoyin Najeriya da kungiyar lauyoyi NBA ta shirya sakamakon janye gayyatar da aka yiwa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i.
A zantawar sa da manema labarai a Kaduna ranar Asabar, shugaban kungiyar, Abbas Masanawa, ya bayyana cewa shawarar da uwar kungiya ta yanke kan janye gayyatar da tayi El-Rufa’i bisa wasu zarge-zarge marasa tushe ba tare da kyautata masa zato ba nuna bangaranci ne na addini da kabila.
Musulman lauyoyin sun ce shin kungiyar NBA ta makance ne lokacin da ake yiwa mutane kisan kiyashi a jihohi irinsu Katsina, Zamfara, Neja da Birnin Gwari a Kaduna, amma sai yanzu idonsu ya bude da na kudancin Kaduna.
Ƙungiyar lauyoyin Musulman tace ta yaya za’a janye gayyatar El-Rufa’i amma a bar gwamnan Rivers, Nyesom Wike, wanda yayi ikirarin cewa jiharsa ta Kirista ce.
“Dubi ga wannan shawara na takaici da uwar kungiyar NBA ta yanke, Kungiyar Lauyoyi Musulmai na jihar Kaduna basu da wani zabi face umurtan mambobinta da su janye daga halartan taron gangamin NBA kuma tana kira ga lauyoyi Musulmi a Najeriya su bi sahu.”
“Kungiyar Lauyoyi Musulmai na Kaduna na jaddada goyon bayansu ga gwamna Nasir El-Rufa’i a yunkurinsa na kawo karshen matsalar tsaro a jihar Kaduna , musamman kudancin Kaduna.”
A ranar Alhamis, Kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) ta janye gayyatar da ta yi wa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, zuwa wurin babban taronta bayan wasu daga cikin mambobin kungiyar sun nuna rashin amincewarsu.
NBA, wacce ta saka sunan El-Rufa’i a cikin manyan baki da za su gabatar da jawabi a wurin taron, ta sanar da cewa ta janye gayyatar da ta yi masa a shafinta na Tuwita a ranar Alhamis.