Kaduna: Kungiyar NURTW Ta Tallafawa Direbobi 360

IMG 20240301 WA0036

Daga Ibrahim Ammani

Kungiyar direbobin sufuri ta kasa NURTW reshen jihar Kaduna ta tallafawa direbobi 360 da kudi naira miliyan 3 da dubu 600 da kuma atamfofi da shaddoji domin rage musu radadin rayuwa.

Kungiyar tace daga ciki akwai mata guda 21 da suka amfana da tallafin wanda hakan Yana daga cikin matakan da kungiyar take dauka na tallafawa rayuwar direbobi.

A jawabin da ya gabatar shugaban kungiyar na jihar Kaduna Alhaji Aliyu Tanimu Zaria, (Magajin Makaman Gusau) yace sun bayar da tallafin ne ga direbobi wadanda suka sadaukar da rayuwar wajen sana’ar tuki yanzu karfin ya kare da kuma direbobi wadanda suka rasu suka bar iyalansu.
Alhaji Tanimu Zaria wanda kuma shine shugaban kungiyar NURTW na shiyyar Arewa Mason yamma yace burinsu shine su tallafawa rayuwar direbobi a duk inda suke.
Shugaban yace bayan dogon nazari da suka yi , sun zakulo direbobi daga shiyyoyi guda uku ma jihar kaduna wadanda suka hada da shiyyar Arewaci da kudanci da kuma tsakiyar jihar Kaduna domin basu tallafin wanda a cewarsa, shine irinsa na farko a fadin kasar nan baki daya.

‘Zamu tabbatar da cewa mun kafa tarihi a kungiyar NURTW wanda mutane da zasu manta damu ba”

“Mun duba munga cewa akwai direbobi sun da dade suna tuki da kuma wadanda suka rasu suka bar mata da yara muka zakulosu domin tallafa musu da abinda zasu San kungiyar tana sane da su kuma tana tare su. Insha Allah duk wadanda muka talkafawa zasu koma gida suna masu farin ciki”

” Wannan shiri da muka fara yanzu samin Tabine saboda yanzu muka fara kuma insha Allah zamu ci gaba da bayarwa babu tsayawa lokaci bayan lokaci”

“Muna da kyakkyawar tunani da tanadi akan direbobinmu a jihar kaduna domin a jihar Kaduna muna tafiya a dunkilene uwa daya uba daya”
Shugaban ya bayyana kudirin kungiyar NURTW wajen inganta rayuwar direbobi da iyalansu baki daya.
A nasa jawabin tsohon shugaban kungiyar NURTW na jihar Kaduna Alhaji Alhassan Haruna 313, yace bayyana gamsuwarsa dangane da matakin da kungiyar ta dauka na inganta rayuwar direbobi da iyalansu.
Alhassan 313 wanda shine shugaban kungiyar direbobi manyan motoci na kasa, ya ce irin yunkuri da shugaban sufuri na jihar Kaduna Aliyu Tanimu Zariya zai takmaka wajen bunkasa ci gaban kungiyar inda ya bayyana gansuwarsa da shirin.
A nada jawabin, Sakataran kungiyar Barure Yusuf Suleman, ya bukaci daukacin ‘ya’yan kungiyar da su ci gaba Bawa shugabannin kungiyar goyon bayan da suka kamata domin aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban kungiyar baki daya.
Bature Suleiman, yace nan da bayan sallah karama kungiyar zata raba motoci da babura ga mambobinta domin ci gaba da last Roman mulkin Alhaji Aliyu Tanimu Zaria .

Labarai Makamanta

Leave a Reply