Kaduna: Kowane Mazaunin Jihar Zai Dinga Biyan Harajin ₦1000

Daga shekara mai zuwa ta 2021, ko wane mazaunin Jihar Kaduna baligi zai dinga biyan kudin haraji Naira dubu daya (₦1,000) a kowace shekara.

Shugaban Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Jihar Kaduna (KADRIS), Dr Zaid Abubakar ne ya sanar da manema labarai hakan a Jihar Kaduna, ya na mai cewa biyan kudin harajin ya samu sahalewar sashi na 9 (2) na dokar garambawul da bunkasa kudaden shiga na jihar Kaduna ta 2020 (Kaduna State Tax Codification and Consolidation Law).

Dr Zaid ya ce dokar ta tanadi kowane mazaunin Kaduna baligi da ya biya ₦1,000 a kowace shekara a matsayin harajin bunkasa jihar Kaduna. A cewar shi, yin haka zai taimaka wa gwamnati wajen samun karin kudaden shiga don ci gaba da gudanar da muhimman aiyukan sauya fasali tare da bunkasa rayuwar al’umar Jihar Kaduna.

Dr Zaid ya kara da cewa Hukumar KADRIS da Kananan Hukumomi da sarakuna ne za su dinga karban harajin a madadin gwamnatin Jihar Kaduna, Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nigeria (NAN) ya ruwaito. A cewar shi nan ba da dadewa ba ne gwamnati za ta fitar da tsare-tsaren yadda aikin karbar harajin zai gudana a fadin Jihar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply