Babbar Kotun Koli dake Kaduna ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Daniel Kaliyo ta tabbatar da kujerar majalisar dokokin tarayya ta ƙaramar Hukumar Lere ta jihar Kaduna ga zaɓaɓɓen ɗan Majalisa na jam’iyyar APC Suleiman Aliyu Lere.
Alƙalin ya bayyana cewa bayan dogon nazari da binciken Kotun, ya tabbata cewar ɗan takarar jam’iyyar PDP da ke kan Kujerar Honorabul Muhammad Rabi’u ba shine halastaccen ɗan Majalisar ba, inda nan take Kotu ta kwace Kujerar ta miƙawa Suleman Lere wanda tun asali shine jama’ar ƙaramar Hukumar Lere suka zaba.
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala zaman Kotun, Injiniya Suleiman Lere, wanda ake wa lakabi da suna “Gari Ya Waye” ya godewa Allah, sannan ya yi godiya ga jama’ar ƙaramar Hukumar Lere bisa addu’o’i da goyon bayan da suka ba shi, har Allah ya sa ya yi nasara.
Zaɓaɓɓen ɗan Majalisa ya kuma yi alƙawarin ɗorawa akan ayyukan da ya faru na cigaba a majalisa, domin ɗaga darajar ƙaramar Hukumar Lere da jama’ar baki ɗaya.
Injiniya Suleiman Lere ya yi nasara a zaben ɗan Majalisar wakilai mai wakiltar ƙaramar Hukumar a zaben da aka yi na shekarar 2019.
Daga bisani wata Kotu a birnin tarayya Abuja ta ƙwace Kujerar ta ba ɗan takarar PDP Muhammad Rabi’u tsawon shekara guda kenan, kafin yanke hukuncin da Kotun koli ta Kaduna ta yi a ranar Laraba inda ta tabbatar da nasarar shi.