Kaduna: Kin Biyan Wadanda Aka Dauko Haya A Taron Atiku Ne Silar Rikici – APC

Rahoton dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki ta dora laifin tarzoma da ta tashi yayin da PDP suka je kamfen din ‘dan takarar shugabancin kasa, Atiku Abubakar a jihar kan jam’iyyar ta PDP.

A yayin martani kan takaddamar a ranar Laraba, sakataren hulda da jama’a na APC na kasa, Felix Morka, ya kwatanta lamarin da ya faru da ja wa kai. “PDP bata da wanda zata dorawa laifi sai kanta a rikicin da ya barka yayin kamfen dinta a Kaduna.

Lamarin a takaice na mutanen da suka dauko haya ne suka jibge, sannan daga bisani manajojin gayyar da suka tsere basu biya su kudinsu ba.

“A maimakon su sunkuyar da kansu cikin kunya da kuma abun ashsha da suka yi a Kaduna, PDP tana neman wadanda zata dorawa alhakin shirmen da suka yi. “A bayyane yake, APC bata da hannu a harin da PDP ke neman manna mata. Ba mu da wani dalili da gangaminsu zai tada mana hankali a kai.

“A matsayinmu na jam’iyyar da tafi kowacce a Afrika, tana tunkaho da nasarorin shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da makomarta karkashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Ba wai PDP ba dake fama da kanta.

“Ko ba komai, PDP ce ta shirya kamfen dinta a Kaduna a ranar da ‘dan takararmu ya ziyarci Kaduna don tattaunawa da DattawanArewa. “Da ace kamfen din haddade ne da sun gujewa haduwar manyan taruka biyu a wuri daya kuma a rana daya.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply