Kaduna: Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-Zanga A Hanyar Abuja

IMG 20240229 WA0296

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa jami’an tsaro sun tarwatsa fusatattun masu zanga-zanga da suka tare babban titin Kaduna zuwa Abuja a ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu.

Majalisar tsaro ta jihar Kaduna ta kuma gargadi masu zanga-zangar kan toshe hanyoyi da cin zarafin bayin Allah da basu ji ba basu gani ba da sunan zanga-zanga.

Matasan dai sun yi zanga-zanga ne don nuna fushinsu kan harin da ‘yan bindiga suka kai Unguwan Auta a Gonin Gora, karamar hukumar Chikun a kwanakin baya.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya saki, ya ce mambobin majalisar tsaron sun tarwatsa shingayen da aka kafa, daga bisani kuma suka bude hanyar domin masu motoci.

Aruwan ya kara da cewa a lokacin da suke zantawa da shugabannin al’umma, mambobin majalisar tsaro na jihar sun nuna rashin gamsuwarsu da barazanar da ke tattare da toshe hanyoyi. Sun ce yin hakan tauye hakkin ‘yan kasa da matafiya da ke amfani da hanyoyin ne.

Labarai Makamanta

Leave a Reply