Kaduna: Iyaye Sun Roƙi El Rufa’i Ya Buɗe Makarantu

Wasu iyaye da dalibai a jihar Kaduna sun yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasiru Ahmad El Rufa’i ta bi umurnin gwamnatin tarayya na bude makarantu.

Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta bada umurnin bude makarantu ranar 12 ga Oktoba, bayan rufesu tun watan Maris sakamako bullar cutar COVID-19.

Amma kwamishanan ilimin jihar, Dr Shehu Makarfi, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba zata bude makarantu ba har sai an kammala binciken tabbatar da cewa rayukan yara ba ya cikin hadari.

“Zamu sanar da lokacin da za’a bude makarantu muddin muka kammala dukkan shirye-shirye domin tabbatar da lafiyan yaranmu,” .

Amma wasu iyaye da dalibai, wadanda suka yi hira da kamfanin dillancin labarai ranar Laraba a Kaduna sun bayyana damuwarsu kan jinkirin da gwamnatin jihar keyi.

Wani mahaifi mai suna, Grace Emmanuel, wanda mazaunin unguwar Sabon Tasha ne ya bayyana cewa ya yi farin cikin samun labarin cewa jami’o’in jiha zasu koma kuma dalibai na shirin jarabawa.

Ya yi kira da gwamnatin jihar tayi irin hakan wajen bude makarantun firamare da sakandare. “Gwamnatin ta yi matukar kokari wajen dakile yaduwar cutar COVID-19…ya kamata ta misalta irin kokarin kan makarantun gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar, ” “Wadannan yaran sun dade a gida na tsawon kusan shekara daya, kuma ina tunanin hakan ba zai kyautatu ga rayuwar karatunsu ba.”

Wani mahaifin mai suna Bawa Magaji, wanda kuma malamin makaranta ne a Unguwar Rimi, ya ce duk da cewa gwamnatin jihar na la’akari da lafiyan yara wajen bude makarantu, za’a iya kare yara idan aka bi dokokin kariya daga COVID-19.
“Ya zama wajibi muyi abinda ya kamata domin ceton ilimin yara saboda akwai aiki matuka wajen koyar da daliban firamare da sakandare abubuwan da ya kubuce musu,”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply