Kaduna: Hatsarin Mota Ya Laƙume Rayukan ‘Yan Sanda Bakwai

‘Yan Sanda Bakwai ne suka rasa rayukansu a mumunan hadarin mota da ya auku ga jami’an sanda da aka yiwa horo na musamman watau ‘special forces’ a hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Rahotanni sun nuna cewa ba’a san abinda ya sabbaba hadarin ba. Sai dai shaidun gani da ido sun bayyana cewa hadarin ya auku misalin karfe 4:30 na la’asar, kusa da barikin Sojin Jaji, inda Motar dake dauke da ‘yan sanda tayi kuli-kulin kubura.

Wani direban motar haya ‘Sharon’ da ya shaida hadarin, Hassan, ya bayyana cewa: “Mumunan hadari ne saboda na kirga kimanin gawawwakin yan sanda bakwai a tsakiyar titi.”
“Wasu biyu sun yi mugun jikkata yayinda sauran suna tsira.”

Yayin da aka tuntubi kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna ASP MUhammad Jalige, ya ce an tura ‘yan sanda wajen domin ganin ainihin abinda ya faru.

Labarai Makamanta

Leave a Reply