Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki kokarin babban bankin Najeriya na sauya wasu takardun Naira inda ya kwatanta lamarin da halaka kai ta fannin tattalin arzikin ‘yan Najeriya balle mazauna kauye.
Gumi ya ?ara da cewar kashi 80 na ‘yan Najeriya mazauna kauye ne kuma sun dogara da tsabar kudi domin siye da siyarwa a dukkanin harkokin su na yau da kullum.
Gumi yace duk wani tsari da zai takura zagayawar kudi tsabarsu tsakanin jama’a zai zama tamkar ibtila’i ga kasar. Ya kara da yin bayanin cewa tsarin ba zai taba hana masu garkuwa da mutane kudi tsabarsu ba saboda zasu iya yanke hukuncin karbar kudin fansa a dala da sauran kudaden ketare kuma hakan ya matsantawa rayuwar jama’a.
“Mutanen dake siyar da kayayyaki zasu fada maka cewa da yawan ‘yan Najeriya basu da kudi, don haka ‘yan kasuwa suna ta tafka asara. A wannan wurin duk abinda zai kawo tsaiko ga yawon kudi zai zamo ibtila’i a kasar nan.
“Da yawan hukunci masu kyau ana aiwatar dasu ne a lokacin da bai dace ba. Akwai yuwuwar wannan zai kasance wani. Duk dai yadda wadanda suka kawo tsarin zasu kuranta shi, amfanin dai ba kamar yadda ake tsammani bane tunda halin da ake ciki na bayyana rashin dacewar shi.
“Kashi 80 na ‘yan Najeriya musamman ‘yan kauye suna amfani da tsabar kudi ne, kwatsam ana komawa amfani da kudin da ba tsaba ba yana nufin karuwar talauci a cikin kankanin lokaci. Idan da akwai amfanin irin hakan, yana zuwa ne bayan shekaru masu yawa na matsanancin talauci da matsin rayuwa wanda babu gwamnati mai fatan alheri da ya dace ta mika mulki a hakan.
“Da a ce an fara tun 2015, hakan na iya zama daidai tunda gwamnatin ce zata dandana kudarta kan hakan. Mu shaida ne kan hana achaba, siyar da fetur da datse sadarwa a jihohin da ‘yan bindiga suke cin karensu babu babbaka. Hakan bai shawo kan komai ba sai dai azabtar da jama’a.