Kaduna: Farashin Kayan Abinci Ya Faɗi Warwas

A yayin da al’ummar Najeriya kokawa kan tashin farashin kayan abinci, farashin kayan abinci ya fadi da kamar kashi 30 a babbar kasuwar hatsi ta garin Saminaka da ke Jihar Kaduna.

Shi dai wannan yanki na Saminaka, shi ne kan gaba a wajen noman masara a Najeriya.
Binciken da Aminiya ta gudanar a kasuwar hatsin da ke ci a kowace ranar Laraba, ya gano farashin kayan abincin ya fadi kasa warwas.

Wakilinmu ya gano cewa buhun sabuwar masara da ake sayarwa kan N15,000 mako biyu da suka gabata, yanzu ta komo N10,000 zuwa 12,000.

Har’ila yau buhun shinkafa mai bawo sabuwa da ake sayarwa N17,000 zuwa N18,00 mako biyu da suka gabata ya dawo N12,000 zuwa N13,000.

Buhun tsabar shinkafa sabuwa mai cin mudu 80, da ake sayarwa kan N49,000 zuwa N50,000 mako biyu da suka gabata ya dawo N32,000 zuwa N35,000.

Bangaren farashin mudu-mudu kuwa, mudun shinkafa da ake sayarwa kan N700 zuwa N750 ya dawo N450.

Mudun masara da ake sayarwa kan N300, makonni biyu da suka gabata, yanzu ya dawo N150.

Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan al’amari, Sarkin Hatsin Saminaka, Manu Isah, ya bayyana cewa tabbas farashin kayan abinci ya sauka a kasuwar ta Saminaka.

Ya ce abin da ya kawo faduwar farashin kayan abincin yanzu shi ne shigowar kayan abinci da yawa, saboda gabatowar kaka.

Ya ce yanzu gari an fara girbe amfanin gona, shi ya sa farashin kayan abincin ya fadi.

“A yau Laraba mun sami baki masu sayen kayan abinci daga wurare daban-daban na Najeriya, kuma akalla an tayar da manyan motocin tirela sama da 10, banda kananan motoci dauke da masara daga wannan kasuwa’’.

Labarai Makamanta