Kaduna: El Rufa’i Ya Yi Wa Tulin Fursunoni Afuwa

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai a ranar Alhamis ya sanar da sakin tarin fursunoni, da rage wa’adin wasu ciki har da waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa da aka sauya musu zuwa ɗaurin rai da rai.

Gwamnan ya sanar da hakan ne cikin jawabinsa na bikin ranar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ƴanci.

“A yayin da muke bikin cika shekaru 60 da samun ƴancin kai, al’adda ce yin afuwa ga wasu da ke gidan gyaran hali a jihar Kaduna. “Don haka, za a saki fursunoni 25, wasu kuma an rage musu wa’adinsu ciki har da ƴan fashi da aka yanke wa hukuncin kisa da aka sauya musu zuwa ɗaurin rai dai rai.”

A bangarensa, Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau a ranar Alhamis shima ya yi wa fursunoni biyar afuwa ciki har da wani Obinna John da aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

A cewar gwamnan John wadda ya riga ya yi shekaru 8 a gidan yari an masa rangwame daga hukuncin kisa zuwa shekaru 21 a gidan yari.

Labarai Makamanta

Leave a Reply