Kaduna: El Rufa’i Ya Yi Wa Fursunoni Huɗu Afuwa

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamna Mallam Nasir El-Rufai na jihar ya yafewa wasu fursunoni hudu a bikin tunawa da ranar ‘yancin kan Najeriya karo na 62 bisa ikon da kundin tsarin mulkin kasa ya bashi.

A cikin wata sanarwa da aka fitar daga gidan gwamna na Sir Kashim Ibrahim, an bayyana sunayen mutanen hudu da gwamnan ya yafewa, waɗanda suka hada da Abdullahi Haruna, Usman Ahmed, Mohammed Sani da Khalillullahi Mohammed.

Sanarwar ta bayyana cewa, an yafewa fursnonin hudu ne saboda tausayinsu da gwamna ya ji, kuma hakan ya dace da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Hakazalika, an ce gwamnan ya yi amfani da shawarin kwamitin yafiya na jihar kafin yanke wannan hukunci. Sanarwar ta ce: “Wadanda aka yafewan suna kan zaman gidan kaso ne na tsawon shekaru uku da ‘yan kai, kuma suna da sauran watanni shida ne ko kasa a gidan yari.

“Gwamna El-Rufai ya bukaci fursunonin da aka yafewa da su kasance masu dabi’a mai kyau yayin da suka koma ga danginsu kuma ga sauran al’umma.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply