Kaduna: El Rufa’i Ya Rushe Makarantar Da Ake Lalata Da ‘Yan Mata

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, ya rushe makarantar Liberation Collage dake cikin garin Kaduna bayan an samu mai makarantar Mista Samuel Ejikeme da laifin yi wa yarinya ‘yar shekara tara fyade.

Wani dalilin da ya kara tunzura gwamnatin yin rushe makarantar kamar yadda wani hadiminsa a fannin yada labarai Abdallah Yunus Abdallah ya bayyana, shine rashin samun sahalewar gwamnati kafin gina makarantar. Kazalika aka samu Mista Samuel na amfani da makarantar wurin lalata yaran mutane.

Labarai Makamanta

Leave a Reply