Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar ƙarkashin jagorancin Gwamna Nasiru El Rufa’i ya bayar da umarnin rushe kasuwar ‘yan canjin kudi dake tsakiyar birnin, inda aka mayar da wurin kufai.
Wakilinmu da ya ziyarci wurin ya gane wa idanuwan sa yadda manyan motocin rusa gine-gine suka rinƙa rusa manyan shaguna da Ofisoshin ‘yan kasuwar na canji ba sassautawa.
Sai dai a zantawar da akayi dashi Shugaban Kasuwar ‘yan Canji na Kaduna Alhaji Ɗalhatu Jumare ya bayyana rusa wajen neman abincin nasu da aka yi a matsayin ƙaddara, kuma matsayin su na musulmi sun yi imani da ƙaddara.
Gwamna Nasiru El Rufa’i dai ya yi kaurin suna wajen rushe gine-ginen dalilin da ya sa ake yi mishi lakabi da Gwamna mai Rusau.