Kaduna: El Rufa’i Ya Ba ‘Yan Hausa Fim Katafaren Fili

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ba masana’antar Kannywood katafaren fili da ya kai girman murabba’i 8,000 domin gina sinima ta zamani a Kaduna.

An ba su filin ne a yankin Doka na Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, inda ake kira da cikin garin Kaduna.

Furodusa Abdul Amart Mai Kwashewa ne ya sanar da hakan, inda ya ce, “Alhamdulillah!

“A cikin alkawarurrika da gwamnatin APC ta yi mana don inganta masana’antarmu ta Kannywood, muna mutukar godiya ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i bisa cika nasa alkawarin na ba mu fili mai fadin murabba’i dubu 8 (8thousand square meters) domin gina babbar sinima ta zamani, da kuma gudunmawar kudi na fara iza harsashi.

“Sannan muna godiya ga Alhaji Musa Halilu (Dujiman Adamawa) bisa jagorantar tabbatuwar wannan al’amari. Allah Ya saka da alheri.

“Muna mika godiya ta musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin APC”.

Kannywood ta dade tana fama da matsalar tabarbarewar kasuwancin fina-finan, wanda hakan ya sa dole wasu masu shirya fina-finan suka jingine harkar, wasu kuma suka koma amfani da manhajar YouTube.

Masu sharhi a kan al’amuran masana’antar da dama suna ganin idan aka samar da sinimomi na zamani da dama, za a iya shawo kan lamarin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply