Gwamnatin jihar Kaduna ta umurci ma’aikatan jihar Kaduna su koma bakin aiki ranar Litinin, 20 ga Yuli bayan kwashe watanni uku sun zaune a gida sakamakon bullar cutar Coronavirus.
Gwamnatin ta sa dokar kulle tun ranar 26 ga Maris, 2020, A takardar da ta fito daga ofishin shugaban ma’aikatan jihar, an zabawa kowani sashen ma’aikata ranakun da zasu rika zuwa aiki daga karfe 9 na safe zuwa 3 na rana.
Takardar da Sakataren din-din-din na ofishin shugaban ma’aikata, Ibrahim Jere, ya rattafa hannun, an umurci dukkan diraktoci, sakatarorin da manya jami’ai su rika zuwa daga ranar Litinin zuwa Juma’a.
Amma ma’aikatan da ke daraja ta 14 zuwa sama za su rika zuwa aiki cikin kwanaki uku; Litinin, Laraba da Juma’a.
Su kuma ma’aikata dake daraja ta 7 zuwa 13 zasu rika zuwa aiki ranar Talata da Laraba kacal.
Bugu da kari, domin takaita yiwuwar yaduwar cutar Korona a ma’aikatun, za’a hana baki ziyara kuma za’a tantance kowani ma’aikaci kulli yaumin tsakanin karfe 8:30 zuwa 9:30 kafin shiga aiki.
Hakazalika za’a tabbatar da bin sharruda irinsu bada tazara, duba zafin jiki, tsafta, wanke hannu da sauran su.