Biyo bayan gama gyaran dokar manyan laifuffuka ta 2017 mai lamba ta 5 sashe na 258 da majalissalar dokokin Jihar Kaduna ta yi, gwamna ya sanya hannu, wacce ta tanadar da hukunci mai tsauri na kisa tare da danda?a ga masu aikata laifin fya?e a Jihar Kaduna;
Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufa’i tare da Uwar Gidansa, Hajiya A’isha Ummi Garba Ahmad El-Rufa’i sun yi taro tare da dukkan manyan jagororin ya?i da matsalar ta fya?e domin tattaunawa kan yadda za a cigaba da aiwatar da tsare-tsaren da za su tainaka wajen magance matsalar ta fya?e gaba?aya musamman ma cin zarafin mata da yara ?anana.
A cikin jawabin da ya gabatar a ya yin taron, gwamna El-Rufa’i ya yabawa uwar gidan nasa Hajiya A’isha Ummi Garba El-Rufa’i bisa goyon bayanta da ?o?ari da jajircewarta kan fafutukar ?wato ?anci da ba da kariya ga mata da yara ?anana wa?anda aka ci musu zarafi ta hanyar lalata.
Daga nan gwamnan ya ?ara da yabawa ma’aikatar ayyukan al’umma da samar da cigaba dangane da ayyukansu na ya?i da dukkan wani cin zarafi da kyautata rayuwar al’umma ha?i da ?o?arin kawo ?arshen fya?e da cin zarafin jinsi.
Baya da haka, gwamna El-Rufa’i ya kuma yabawa hukumomin duniya da ?ungiyoyin sa kai a cikin gida da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudunmawar da su ke bayarwa wajen ya?i da matsalar fya?e da cin zarafin ?an adam a Jihar Kaduna.
Daga ?arshe gwamnan ya kuma ba da tabbacin gwamnatinsa na cigaba da yin duk mai iyuwa wajen ba da goyon baya domin ganin an kawo ?arshen matsalar tare da tabbatar da hukunci ga duk wa?anda aka kama da aikata laifin.
Ita ma a nata jawabin, uwar gidan gwamnan, Hajiya A’isha Ummi Garba El-Rufa’i ta yabawa dukkan ?an gwagwarmaya masu fafutuka wajen ya?i da matsalar. Daga nan ta kuma ?ara da jan hankalinsu da su cigaba da ha?a kai su kauda duk wani sa?ani da bambance-bambance a tsakani domin ganin an magance duk wani nau’in cin zarafi da lalata rayuwar ?a?a mata da yara ?anana a Jihar Kaduna. Inda daga ?arshe kuma ta hore su da su cigaba da tafikar da aikinsu bisa tsari da ?warewa.
Mahalarta taron sun ha?a da:
- Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufa’i
- Uwar gidan gwamna, Hajiya A’isha Ummi Garba El-Rufa’i.
- Lauyar gwamnatin Jiha, A’isha Dikko
- Kwamishin ayyukan al’umma Hafsat Mohammed Baba
- Shugabar shirye-shirye na (UNFPA) na shiyar Arewa maso Yamma, Maryama Darboe.
- Shugabannin manyan ?ungiyoyin sa kai masu fafutukar kawo ?arshen matsalar fya?e da cin zarafin al’umma a Jihar Kaduna.