Kaduna: Babu Bukukuwan Sallar Layya – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya amince da yin sallar idin babbar sallah a fadin jihar. Gwamnan ya sanar da hakan ne a tattaunawar da yayi da manyan gidajen rediyon jihar Kaduna wanda aka fara da karfe 8 na daren ranar Alhamis.

Ya ce sharadin yin sallar idin shine tabbatar da cewa an yi shi a fili sannan a kiyaye dokokin dakile yaduwar annobar korona. Gwamnan ya bukaci dukkan masallatan da su garzaya gida bayan kammala sallar idin.

Bai amince da yin shagalin bikin sallar ba. Kamar yadda yace, “Na amince da yin sallar Idi a fadin jihar Kaduna amma a fili kuma tare da kiyaye dokokin dakile yaduwar COVID-19.

“Ana bukatar jama’a da su koma gida bayan kammala sallar amma ba a amince da su yi wani bikin shagalin sallah ba wanda za a tara taro.”

A jawabin mataimakiyar gwamnan jihar, Hajiya Hadiza Balarabe, ta yi kira ga mazauna jihar da su kasance ‘yan kasa nagari. Ta bukacesu da su rungumi zaman lafiya tare da bada himma wurin kiyaye kai.

Saka takunkumin fuska, zaman gida, nesa-nesa da juna, tsaftar numfashi, wanke hannuwa da sabulu da ruwa, gujewa taron jama’a masu yawa da cin abinci mai lafiya zai taimaka, wajen daƙile cutar inji ta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply