Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Kaduna: An Yi Nasarar Hallaka Kwamandan ‘Yan Bindiga Dogo Maikasuwa

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Sojoji sun kashe wani jagoran ‘?an Bindiga a jihar mai suna Dogo Maikasuwa.

Wata sanarwa da kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar, Samuel Aruwan ya fitar, ranar Juma’a, ta ce an hallaka Maikasuwa ne lokacin da dakarun suke sintiri a ?aramar hukumar Chikun.

Sanarwar ta ce jami’an tsaron sun samu nasarar ?wato bindiga ?aya ?irar AK-47, da alburusai, da babura biyu da kuma kayan sojoji.

Ta ?ara da cewar Dogo Maikasuwa, wanda ake kira da Maimillion ya jagoranci kai hare-hare da garkuwa da mutane masu bin hanyar Kaduna zuwa Kachia da kuma wasu kauyuka na ?aramar hukumar Chikun.

Exit mobile version