Kaduna: An Yi Nasarar Hallaka Kwamandan ‘Yan Bindiga


Gwamnatin jihar Kaduna ?ar?ashin jagorancin Gwamnan jihar Nasiru Ahmad El Rufa’i ta tabbatar da kisan da aka yi wa daya daga cikin shugabannin kuma gagararren dan bindiga mai suna Rufai Maikaji tare da sama da ‘yan bindiga dari dake karkashinsa.

Labarin mutuwar Maikaji ta fasu ne bayan kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar da ita a wata takardar sanarwa da aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna.

Kamar yadda takardar ta sanar, Maikaji tare da daruruwan ‘yan bindiga sun sheka lahira bayan samamen da sojin sama suka kai a dajin Malul da ke karamar hukumar Igabi ta jihar.

Wani sashi na takardar na cewa: “Samamen da sojin saman Najeriya suka kai a karshen watan Fabrairun da ta gabata sun yi nasarar halaka Rufai Maikaji da gungun ‘yan bindiga dake karkashinsa.

‘Yan bindigan sun tsere zuwa kauyen Anaba da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna bayan ganin sojojin kasa. Na saman sun gaggauta yi musu ruwan wuta wanda hakan ya kawo karshen Rufai Maikaji da mukarrabansa.”

Related posts

Leave a Comment