Kaduna: An Tarwatsa Makarantun Allo A Birnin Zazzau

An wayi gari a yau litini inda acikin garin Zaria Jahar Kaduna, gamayyar Jami’an Tsaro suka dunga zagayawa lungu da sako domin farautar makarantar da aka tabbatar na almajirai ne, ana ta kakkamasu.

“Bugu da kari inda jami’an suka rika kamo almajirai suna sanya su a Mota, zuwa garuruwansu, tareda yima malaman makarantar gargadin gujema Tara Aljamirai, idan kuma kunne yaki ji Gwamnati zata rushe duk ilahirin makarantar, kamar yanda jami’an tsaron suke shelan hakan.

Bayan sun loda almajiran a mota, cikin almajiran harda marasa Lafiya, inda aka rika sanyasu ga motan ‘Ambulance’ Dan Neman masu Lafiya karkashin kulawar Gwamnatin Jahar Kaduna, kamar yanda mai rahoto ya labarto mana hakan daga Wannan wurin da abubuwan yake faruwa.

“Abin baifa tsaya a nan ba, inda jami’an tsaron suka rika bi cikin kasuwan Zaria, suna umarni ga duk masu Sayar da abubuwa dasu dunga rufe kayayyakinsu, musamman ga wadanda suke Sayar da abubuwan ci da sha, domin gujema karuwar cututtuka a fadin jahar.

Related posts

Leave a Comment