Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ma’aikata a jihar sun shiga cikin firgici da tashin hankali sakamakon matakan da gwamnatin Jihar ?arkashin Jagorancin El Rufa’i ta dauka na rage yawan ma’aikata a kananan hukumomin Jihar.
Ma’aikata sun yi ta zubar da hawaye na shiga tashin hankali a sakatariyar karamar hukumar Jema’a dake Kafanchan, jihar Kaduna ranar Laraba yayinda gwamnatin jihar ta mika wasikun sallama ga wasu ma’aikata 82.
Wannan sabon kora ya biyo bayan jita-jitan da aka kwashe makwanni ana yi cewa gwamnatin jihar na shirin rage ma’aikata a kananan hukumomin 23.
Yayinda kamfanin dillancin labarai NAN ya ziyarci Sakatariyar, an ga ma’aikatan rike da takardunsu cikin takaici da bakin ciki.
A cewar wasikar, an yi hakan ne a yunkurin da akeyi na kawo gyara da sauyi kananan hukumomin jihar.
DUBA NAN: Kwamishinan Yan sandan Lagos ya ?auki ?wa?kwaran Mataki don gujema abinda ya faru a Owerri Hawaye sun kwaranya a jihar Kaduna yayinda gwamnati ta sallami ma’aikata 82 nan take da fargabar sake sallamar wasu masu yawa.
Daya daga cikin ma’aikatan da abin ya shafa wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa da wane dalilin gwamnatin za ta dauki irin wannan mummunan mataki a lokaci irin yanzu da mutane ke fama.
“Ta wani dalili gwamnati za ta yi irin wannan abu yanzu. Shin basu san ana cikin halin kunci bane a kasar nan.”
“Da kyar mutane ke rayuwa da dan albashin da suke samu, sannan kuma sai kawai a kwace musu abinci.”
Wani ma’aikacin wanda shima ya bukaci a sakaya sunansa saboda gudun kada a hanashi fansho ya bayyanawa NAN cewa ya rungumi kaddara.