Kaduna: An Shawarci Matasa Su Dage Wajen Neman Na Kansu – Mai Kwai

An Shawarci matasan yankin ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa da jiha baki daya da su dage wajen neman na kansu su rage dogaro da neman aikin gwamnati.

Shawarar ta fito ne daga bakin wani ɗan Kasuwa kuma ɗan siyasa mai suna Alhaji Abdullahi Ibrahim mai kwai a yayin wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a Kaduna.

Mai Kwai wanda ya bayyana Matasa matsayin ƙashin bayan cigaban kowace al’umma, bisa ga haka cigaban su shine cigaban jama’a baki daya.

“Ina son yin amfani da wannan dama in yi kira ga matasa su tuna baiwar da Allah ya yi musu ta hankali da basira, ya kamata su yi amfani da wannan baiwa wajen taimakon kansu da kansu ba jiran wani aiki daga gwamnati ba tun da yanzu aikin gwamnati ya yi wuya, komai kankantar sana’ar ka ka riƙe ta da kyau”.

Daga ƙarshe Alhaji Abdullahi Ibrahim mai kwai ya yi kira ga gwamnati da ta ƙara bada dama ga Matasa wajen cire su daga halin kunci da suke ciki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply