Kaduna: An Kashe ‘Yar Shekara Shida Ta Hanyar Fya?e

An gano gawar wata yarinya ‘yar kimanin shekara shida da aka yi wa fyade kuma aka kasheta, aka jefar a wata makabarta da ke Kurmin Mashi, a Kaduna.

Wani manomi ne dai ya ga gawar yarinyar, lokacin da yake dawo wa daga gona, inda ya yi saurin sanar da jama’ar da ke wuce wa ta wurin.

Shaidun gani da ido ya zuwa lokacin hada wannan labari, sun yi hasashen cewa yarinyar ta dawo daga Islamiyya da misalin karfe 11 na safiyar ranar Lahadi, inda ta sauya kayanta ta fita makwabta wasa, kafin mahaifiyarta, ta lura cewa ‘yar ta bata dawo ba.

Kokarin jin ta bakin mahaifiyar yarinyar ya ci tura, saboda yadda ta fita hayyacinta ganin abun da ya faru da yarinyarta.

Da take magana kan batun, kwamishinar harkokin jama’a da kyautata rayuwa ta jihar Hajiya Hafsat Baba, ta nuna takaicinta kan wannan al’amari, tana mai kira ga ‘yan sanda su yi dukkan mai yiwuwa wajen gano wadanda suka aikata laifin, da kuma kare faruwar hakan a nan gaba.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar ASP Muhammad Jalige, wanda ya tabbatar da gano gawar yarinyar, ya yi gargadi kan yada cewa kashe ta aka yi bayan an yi mata fyade, ba tare da an kammala bincike ba.

A naku shawarar wani irin hukunci ya dace ga masu aikata ire Iren wannan laifuka?

Related posts

Leave a Comment