Kaduna: An Hallaka Shugaban ‘Yan Bindiga Nasiru Kachalla

Mummunan fa?a tsakanin manyan ?ungiyoyin ‘yan bindiga biyu a dokar dajin Birnin Gwari ta Jihar Ka ya yi sanadiyar mutuwar gagarumin ?an bindiga Nasiru Kachalla wanda ya jima yana kisa da garkuwa da mutane a Jihar Kaduna.

Kachalla ne wanda ake zargin shine jigon bayan ayyukan ta’addanci da dama a Jihar Kaduna da kewaye, an tabbatar da rashin tausayin da imanin shi ga bayin Allah wa?anda suka fa?a cikin tarkon shi.

Ana zargin sa da aikata laifukan garkuwa da da dama ciki harda garkuwa da dalibai da malaman makarantar Engraves a Watan Oktoban 2020 na wannan shekarar.

A wata sanarwa da Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida ya fitar ranar Litinin ya ce an kashe Kachalla a wata fafatawa tsakanin tawagar sa da kuma wata tawagar yan ta’addan.

A cewar Aruwan, masu binciken kwakwaf sun tabbatar da cewa an kashe yan ta’addan daya bangaren, da kuma wasu daga cikin sojojin Kachalla. “Karawar ta afku a wani daji da ke kan iyakar kananan hukumomin Kajuru-Chikun na jihar Kaduna,”.

Aruwan ya yi bayanin cewa fadan ya barke akan wani garken shanu da aka sato.
Ya ce Kachalla da tawagar sa suna da hannu wajen ayyukan bata gari, ciki har da garkuwa da mutane, kashe kashe da kuma ta’addancin da ke faruwa kan titin Kaduna zuwa Abuja dama na Chikun/Kajuru.

Kwamishinan ya bayyana cewa Kachalla ne ya shirya garkuwa da mahalarta bitar da aka shiryawa makiyaya ranar 9 ga Janairun 2020 da kuma garkuwa da Mrs Bola Ataga da yayan ta guda biyu ranar 24 ga Janairun 2020.

“Daga bisani kuma ‘yan ta’addan suka kashe daya daga cikin mahalarta taron, Michael Nnadi da Mrs Ataga kafin su saki yayan ta,” a cewarsa.

Tawagar Kachalla ne dai ke da hannu wajen garkuwa da dalibai shida da kuma malamai biyu na makarantar Engravers College, a kauyen Kakau na karamar hukumar Chikun ranar 3 ga Oktobar 2019.

Related posts

Leave a Comment