Kaduna: An Bukaci Kotu Ta Dakatar Da Cigaba Da Aiwatar Da Ayyukan El Rufai

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa wasu al’ummar jihar sun shigar da gwamnati kara gaban kotu inda suke buƙatar a dakatar da gwamnati mai ci da ci gaba da gudanar da ayyukan tsohuwar gwamnatin El Rufai wadanda suka saɓa doka a biranen Zariya, Kafanchan da Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa wani mai suna Mr Yusuf Sule Bobai daga yankin ƙaramar Hukumar Zangon Kataf ne ya jagoranci shigar da ƙarar.

Ƙarar ta haɗa gwamnatin jihar Kaduna da majalisar dokokin jihar inda aka bukaci su dakatar da duk wani yunkuri na aiwatar da ayyukan tsohuwar gwamnatin saboda cin karo da doka.

Ƙarar ta Yusuf Sule Bobai da gwamnatin jihar Kaduna mai lamba KD/KAD/713/2023 a halin yanzu tana gaban mai Shari’a B. Mohammed na babbar kotun Kaduna.

Labarai Makamanta

Leave a Reply