Kaduna: Alkali Ya Bada Umarnin Cigaba Da Tsare Zakzaky

Zaman ba yi tsayi ba. Wakili daga kotun ya tabbatar mana da halartar Lauyoyin Zakzaky, bayan kammala zaman da duba kan kudurin da ake zama akai.

Daga karshe Alkalin kotun ya bayyana ranar 29/9/2020 a matsayin ranar da zai yanke hukuncin kan kudurin, wato nan da kwanaki 53 masu zuwa.

Zakzaky dai na cigaba da rayuwa a gidan jarum tun bayan arangamar da aka yi tsakanin Sojoji da Almajiranshi a shekarar 2015, rikicin dai ya samo asali ne na tarewa Shugaban dakarun sojin Najeriya Janar Buratai hanya da ‘yan Shi’an suka yi, da bijirewa magiyar da sojojin suka yi musu, lamarin da ya haifar da taho mu gama tsakanin bangarorin biyu.

Bisq ga hukuncin da alkalin ya zartar a yau, Madugun ‘yan Shi’an zai cigaba da zama a gidan kaso har ya zuwa karshen watan tara na wannan shekara ta 2020 da muke ciki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply