Kaduna: ?ungiyar Malaman Jami’a Ta Yi Tir Da Karin Ku?in Karatu

?ungiyar Malaman jami’ar jihar Kaduna, sun nuna adawar su ga karin kudin karatun da aka yi a jami’ar Jihar Kaduna, inda suka bayyana wannan mataki da gwamnatin Jihar ?arkashin Gwamna El Rufa’i ta ?auka a matsayin mummunan mataki da zai haifar da tarnaki a fuskar Ilimi.

Kungiyar Malaman jami’a ta ce za a samu raguwar dalibai a makarantar saboda mafi yawan iyayen yaran da ke karatu talakawa ne marasa hali, masu fadi tashi wajen abin da zasu ci sannan su biyawa ‘ya’yan nasu ku?in Makaranta.

Kungiyar ta ASUU reshen jami’ar Jihar Kaduna KASU ta ce iyayen dalibai ba za su iya daukar dawainiyar ‘ya ‘yansu bayan gwamnatin jihar Kaduna ta kara kudin karatun ba, wanda hakan ke nuna cewar za’a samu gagarumar matsala.

Malaman jami’ar sun yi kira ga gwamnatin Nasir El-Rufai da ta janye matakin da ta dauka na yin karin kudi, ta yi abin da ba zai wahalar da marasa karfi ba. Jami’ar KASU ta na da dalibai 19, 000 wanda 17, 000 daga cikinsu daga jihar Kaduna su ka fito.

Shugaban kungiyar ASUU reshen jami’ar ta Kaduna, Peter Adamu ya bayyana wannan a jiya. Adamu ya ce ‘ya’yan talakawa ne duk su ke karatu a KASU. Peter Adamu yake cewa: “Akalla kashi 70% na yaran gida da ke karatu a makarantar ‘ya ‘yan manoma, ma’aikatan gwamnati da kananan ‘yan kasuwa ne.”

“Abin da ya fi muni shi ne gwamnatin jihar ta kori mutane da yawa daga cikin ma’aikatanta, cikinsu akwai iyaye da masu daukar nauyin dalibanmu.” “Wadannan mutane su na wahala ne domin su biya kudin makaranta a wannan yanayin tattalin arziki da ake ciki.

Karin 500% zai sa dubunnai su bar karatu.” Adamu ya ce babu hikima a matakin da aka dauka lokacin da ake fama da satar mutane, sannan ya soki tsarin biya wa dalibai kudin karatu da aka shigo da shi.

Related posts

Leave a Comment