Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Kada Ku Karya Tattalin Arzikin Najeriya Da CORONA – Majalisar Dattawa

Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan da kada su kashe tattalin arzikin Najeriya ta hanyar daukar salon Turawa wurin yaki da annobar korona. Majalisar dattawan ta yi wannan zancen ne a ranar Talata sakamakon sabon salon yaki da cutar korona da aka dauka. Sun samu zantawa tsakanin kwamitin majalisar dattawa da ke kula da sufurin jiragen sama da lafiya, da kuma masu ruwa da tsaki a kan yadda cutar korona ta kasa kamari a Najeriya da sauran kasashen Afrika.

Shugaban kwamitin majalisar, Sanata Smart Adeyemi, ya ce duba da yadda cutar take, ba daidai bane a ce Najeriya na kwaso tsarin yakar cutar daga Turai, Amurka da China. Amma kuma, shugaban kwamitin yaki da annobar na fadar shugaban kasa, Dr Sani Aliyu, ya tabbatar da cewa talauci yana daya daga cikin manyan makaman da suka yaki cutar.

A yayin kara bayani, Sanata Adeyemi ya ce, “Babu wani abu da ke tare da ‘yan Afrika da babu a Turai da Amurka, wanda yasa cutar korona ba za ta iya yi mana mugun illa ba. “A saboda hakan, akwai wasu matakan da bai dace kasar nan ta dauka ba duba da yanayin tattalin arzikinmu gudun halakarsa baki daya.”

Exit mobile version