Ka Yi Gaggawar Buɗe Kasuwanni – Kudan Ga El Rufa’i

Ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar PDP, Hon Isa Ashiru Kudan yayi kira na musamman ga gwamnan Jihar Kaduna da yayi wa Allah ya bude babban kasuwar jihar Kaduna.

Kudan ya bayyana hakan ne yayin zantawa da yan jaridu a yammacin yau inda ya bukaci gwamnantin ta karfafa ganin anbi matakan kariya tun daga bakin kofar shiga kasuwannin tare da sanya matakan ganin anbi dokokin yadda ya kamata

Tun bayan bullar cutar covid 19 gwamnatin jihar Kaduna ta dauki matakan kariya Inda ta sanya dokar zaman gida Wanda shima Ashiru Kudan ya jinjinawa matakan da gwamnatin ta dauka, amman duk da haka ya kamata a bude babban kasuwar sheikh Gumi koda ba a bude sauran kananan kasuwannin ba domin ganin an samu hada hadar kasuwanci a tsakanin talakawa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply