Ka Tausaya Ka Bada Beli Na – Roƙon Magu Ga Shugaban ‘Yan Sanda

Dakatattacen mukadashin shugaban yaki da rashawa ta EFCC, Mr Ibrahim Magu da ake bincika a kan zargin rashawa ya nemi Sufeta Janar na Rundunar Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya bayar da shi beli. Kwamiti na musamman da shugaban kasa ya kafa karkashin jagorancin tsohon alkalin kotun koli Ayo Salami ne ke bincikar Magu. Magu, wanda aka tsare tun ranar Litinin ya rubuta wasika ta hannun lauyansa, Mr Oluwatsosin Ojaomo a ranar Juma’a zuwa ga IG na neman beli kamar yadda The Punch ta ruwaito.

” Tun ranar da aka kama shi, Magu yana tsare ne a wani wurin ajiya na rundunar ‘yan sanda a Abuja inda daga nan ya ke zuwa gurfana gaban kwamitin binciken. Wasikar da lauyansa ya rubuta zuwa ga ofishin IGP mai dauke da kwanan wata na 10 ga watan Yuli kamar yadda majiyar Muryar ‘yanci ta ruwaito ta nemi a bayar da shi beli, “bisa sanayar da aka masa a kasa.”

Kuna goyon bayan bada belin Magu ko kuwa a cigaba da tsare shi har sai an kammala bincike?

Labarai Makamanta

Leave a Reply