Ka Janye Ƙarin Mai Ko Mu Tsauwalawa Fasinjoji – Direbobi Ga Buhari

A yau Asabar Kungiyar direbobi ta kasa wato (NURTW) ta sanarwa manema labarai cewa za su kara kudin mota ga fasinjoji muddin shugaba Buhari bai rage kudin man fetur da gaggawa ba.

Wannan barazana dai ta fito ne daga bakin shugaban kungiyar na jihar Kwara, Alhaji Abdulrazaq Ariwoola kwanaki kadan bayan shugaba Buhari ya kara farashin man fetur da kudin wutar lantarki a duk fadin kasar.

Alhaji Abdulrazaq Ariwoola ya ce bai kamata a irin wannan halin na kunci da talakawa suke ciki gwamnatin ta kara farashin man fetur ba tunda ta san har yanzu al’umma ba su gama farfadowa daga radadin annobar cutar corona virus ba.

Sannan Ariwoola ya ce su kansu direbobi abin zai shafe su tunda ba za su na samun fasinjoji ba saboda tsadar kudin mota kuma hakan ba karamin jikkata talakawa da masu karamin karfi zai yi ba.

Kamar yadda jaridar Punch ta raiwaito cewa Kungiyar ta ce ba wannan ne lokacin da ya kamata gwamnatin ta kara kudin man fetur da na wutar lantarki ba saboda babu wani cigaba da hakan zai kawo sai dai ma ya sake janyo kara tabarbarewa abubuwa ya kuma jefa talakawa cikin halin kaka-ni-kayi.

Daga karshe kungiyar tana kira ga shugaba Buhari da ya yi gaggawar daidaita abubuwa domin talakawa da sauran masu karamin karfi mazauna kauyika.

Shin mene ne ra’ayinku akan wannan barazanar da kungiyar ta yi?

Labarai Makamanta

Leave a Reply