Ka Da Ku Yi Kuskuren Rashin Zabena A Shugabancin Kasa – Tinubu Ga Inyamurai

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, Bola Tinubu ya fada ma Inyamurai a Enugu cewa idan suka zabe shi, zai bari su dandani zuma a kasar. Tinubu ya bukaci al’ummar jahar Enugu da Inyamurai gaba daya da su zabe shi domin su sha romon dadi a gwamnatinsa.

KARA KARANTA WANNAN 2023: Tinubu, Kwankwaso da Obi za su tashi a tutar babu, malami ya hango magajin Buhari 2023: Bani Gishiri In Baka Manda Za Mu Yi Da Inyamurai a Zabe Mai Zuwa, Inji Tinubu Hoto: @officialABAT Asali: Twitter Premium Times ta nakalto Tinubu yana cewa:

“Idan ka zuba jari ne kawai za ka iya girbewa. Idan ku ka zabe ni za ku sha romon dadi a kasar nan”

Da yake magana a Enugu, tsohon gwamnan na jihar Legas ya ce zai daukaka darajar jihar ta zama cibiyar masana’antu fiye da yadda take a yanzu. Ya bayyana kungiyar yakin neman zabensa a matsayin jirgin kasa mai tafiya wanda ya shirya lashe zabe, cewa duk wani yunkuri na tsayawa a gaban jirgin kasa da ke kan tafiya zai kare ne a cikin tashin hankali.

“Ba za ku iya shiga gaban nasara ba. Rashin sani ne kawai zai sa ka yi yunkurin tsayawa a gaban nasara.

Labarai Makamanta

Leave a Reply