Juyin Mulkin Nijar: Tinubu Zai Jagoranci Taron ECOWAS A Abuja

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa shugabannin Yammacin Afrika za su gudanar da wani taron gaggawa a ranar Lahadi don tattaunawa kan juyin mulki da aka yi a Jamhuriyar Nijar a ranar Laraba.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kuma shugaban kungiyar ta ECOWAS zai jagoranci zaman a Abuja, babban birnin Najeriya.

Shugaban kasa Tinubu dai shi ne sabon shugaban kungiyar Ecowas kuma ya yi alkawarin dawo da nahiyar Afirka kan tsari.

Cikin wata sanarwa, shugaba Tinubu ya fitar ya yi Alla-wadai da juyin mulkin, inda kuma ya yi wa al’ummomin kasashen waje cewa zai yi duk mai yiwuwa domin kare dimokuraɗiyya da kuma tabbatar da zaman lafiya a nahiyar Afirka.

Labarai Makamanta

Leave a Reply