Juyin Mulkin Mali: Majalisar Ɗinkin Duniya Za Ta Yi Zaman Gaggawa

Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya za tayi ganawar gaggawa kan lamarin kasar Mali ranar Laraba, kwana daya bayan juyin mulki Sojoji a kasar dake yammacin Afrikan.

Kasar Faransa da Nijar ne suka bukaci a yi ganawar kuma za ta gudana a sirrance ranar Laraba, wani babban jami’in MDD da ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana hakan.

Hakazalika, sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, ya yi Alla-wadai da damke shugaban kasar Mali kuma ya bukaci “a sakeshi ba tare da bata lokaci ba”. “Sakatare Janar ya yi tirr da wannan abu kuma ya yi kira da mayar da halastaccen shugabanci da doka a Mali,”.

A bangare guda, Gamayyar kasashen nahiyar Afrika AU, ta yi Alla-wadai da damke shugaban kasar Mali, Ibrahim Keita da Firam Mininsta Boubou Cisse, da sojojin kasar sukayi.

“Muna masu fada muku cewa shugaban kasa da Firam Minista na hannunmu” Daya daga cikin Sojin ya bayyanawa AFP.

Martani kan hakan, shugaban gamayyar kasashen Afirka, Mousa Faki, ya yi kira ga sakin su biyu ba tare da bata lokaci ba. Hakazalika ya yi kira ga majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyin duniya su nuna rashin amincewarsu da yunkurin amfani da karfin Soja wajen mulki a Mali.

Gabanin damke shugaban kasan a ranar Talata, tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, wanda shine wakilin ECOWAS da aka tura sulhunta rikicin Mali, ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari. Ya bayyanawa Buhari cewa kungiyar adawa a kasar Mali, M5, ta doge kan bakanta cewa sai shugaba Keita ya yi murabus Za ku tuna cewa a watan Yuli, Shugaba Buhari da wasu shugabannin ECOWAS sun kai ziyara kasar Mali domin sulhunta bangarori biyu amma ganawarsu da shugaban hamayya, Imam Dicko, ya kare a baran-baran.

Labarai Makamanta

Leave a Reply