Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban ?asa Goodluck Jonathan murnar cika shekara 63 da haihuwa.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa ta fuskar ya?a labarai Femi Adesina ya fitar ranar Alhamis, Buhari ya ce Jonathan ya janyo wa Nijeriya martaba da ?ima a idon duniya.
Buhari ya ce jajircewa da dattakun tsohon shugaban ?asar a siyasar Nijeriya ce bar ta kai shi ga jagorantar tawagar ?ungiyar ECOWAS ta samar da zaman lafiya a ?asar Mali.
Tsohon shugaba Jonathan dai ya kafa tarihi a yankin nahiyar Afirka kasancewar shi Shugaba na farko da ke kan Karagar mulki da ya amince da shan kaye a hannun abokin hamayyar shi.
A zaben 2015 Jonathan ya amince da shan kaye a hannun Shugaba Buhari, inda ya bayyana cewar ya yi hakan ne domin kariya daga tsare dukiyoyi da rayukan ‘yan Najeriya, wanda ?in amincewar shi na iya haifar da matsala.