Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bai wa ‘yan ƙasar haƙuri game da “jan ƙafar da gwamnati ta yi” kan gyaran ayyukan rundunar ‘yan sandan ƙasar.
Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce yana sane da cewa matasa na cikin fushi game da abin da rundunar SARS take aikatawa “kuma suna da dalilin yin hakan”.
Kusan mako biyu kenan aka shafe ana zanga-zanga a wasu jihohin Najeriya ta yin Allah-wadai tare da kiran da a kawo ƙarshen ayyukan rundunar SARS ta ‘yan sanda, wadda ke yaƙi da fashi da makami sakamakon zargin cin zarafin ‘yan ƙasa da kashe mutane ba tare da shari’a ba.
Tun a ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba ne Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Muhammed Adamu ya sanar da rushe SARS, sai dai har yanzu ba a daina zanga-zanga ba.
“Ya ku ‘yan Najeriya, na sani cewa da yawa daga cikinku ransu a ɓace yake, cewa ya kamata mu ɗauki matakai cikin sauri. Saboda haka muna neman afuwarku,” in ji Osinbajo.
a Najeriya sanye da hijabi?
A ranar Alhamis ne Osinbajo ya jagoranci zaman Majalisar Tattalin Arziki ta Najeriya – wadda ta haɗar da gwamnonin jihohi 36 har da ministan Abuja – inda suka zayyana wasu matakai da za su ɗauka kamar yadda masu zanga-zanga suka buƙata.
Osinbajo ya ce: “Na sani sarai yadda matasa ke ji. Da yawa na jin cewa mun yi gum da bakinmu kuma ba mu yi komai ba. Kuna da dalilin yin hakan.
“Tun daga makon da ya gabata, muna bin zanga-zangar kuma na yi tattaunawa da masu ruwa da tsaki da ya kamata ku sani. Gaskiya na ɗaya daga cikin rukunan gudanar da mulki.”
Daga cikin sakamakon zaman Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa da Osinbajo ya jagoranta, akwai kafa kwamitocin bincike a kowacce jiha da zai zaƙulo waɗanda ‘yan sanda suka ci zarafi “domin yi musu adalci”.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce “na san burinku shi ne ku gani a ƙasa kuma ina faɗa muku cewa ana tsaka da yin aiki”.
Wajibi ne kowacce jiha ta kafa kwamitin shari’a domin binciken cin zarafi da ‘yan sanda suka aikata wanda zai kasance ƙarƙashin shugabancin:
Tsohon alƙalin kotun tarayya
Wakilai biyu daga ƙungiyoyin farar hula
Ɗan sanda ɗaya mai ritaya
Wakilin matasa guda ɗaya
Wakilin ɗalibai guda ɗaya
Wakilin antoni janar na jihar guda ɗaya
Wakili guda ɗaya daga Hukumar Kare Haƙƙi ta Ƙasa
Aikin kwamitin
Karɓa tare da bincika ƙorafin cin zarafi ko kisa da ‘yan sanda suka aikata
Tantance shaidu da aka gabatar tare da tabbatar da gaskiyarsu
Bayar da shawarar biyansu diyya da kuma matakin gyara da za a iya ɗauka
Kwamitin zai gudanar da aikinsa ne cikin wata shida – sai dai idan gwamna na da wani ƙwaƙƙwaran dalili na tsawaita shi
Kazalika, majalisar ta umarci kowanne gwamna da ya kafa wata gidauniya mai suna Victims Fund da za ta biya waɗanda aka ci zarafi diyya.
Mataimakin shugaban na Najeriya ya ce babu wani ɗan sanda da ya yi aiki a SARS da za a sanya a cikin sabuwar rundunar SWAT.
BBC HAUSA