Jin Ƙan Al’umma: Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Kwamitin Ƙwararru

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da kwamitin kwararru mai mutum 27 kan aiyukan jinkan al’ummar kasa (NHCTWG) domin samar da goyon bayan kwararru ga kwamitin kula da aiyukan jin kai na kasa (NHCC) wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin kula da dukkanin aiyukan jinkai da agaji a fadin kasar nan.

Ministar harkokin Jinkai, kula da ibtila’i da bunkasa walwalar jama’a Hajiya Sadiya Umar Farouk ita ce ta kaddamar da kwamitin, da samar da tsare-tsaren da suka dace domin kyautata aiyukan jinkan al’umman Nijeriya da irin aiyukan da kwamitin zai gudanar.

Sadiya ta kalubalanci mambobin kwamitin da su tabbatar da aiwatar da dukkanin shawarorin NHCC da suke da alaka da tsarin CiSEC don fitar da tsararren tsarin gudanar da aiki tare da ka’idoji gami kuma da sanya hangen nesa kan aiyukan da suka shafi jin kai da tallafa wa al’umman Nijeriya.

Bugu da kari kuma, ta ce baya ga shiyyar arewa maso gabas, akwai bukatar kwamitin ya kuma yi la’akari da dukkanin fadin kasar nan wajen gudanar da aiyukansa da suka dace.

Ta kuma nemi kwamitin da ya shigo da dukkanin wadanda abun ya shafa musamman wadanda suke da wani sani kan shawo kan rigingimu tare da lura da batun tsaro da ya shafi kasa.

A cewar Ministan tabbatar da samar da aiyukan hadaka da ma’aikatarta da bangarorin tsaro zai yi matukar taimaka musu wajen sauke nauyin da ke kawunansu na tallafa wa al’umman Nijeriya har ma da rage kaifin fadawa cikin bala’o’i ta fuskacin kula da kayayyakin da aka samar da wadanda ake raba wa al’umman kasa.

Kwamitin wanda Grema Ali ke shugabanta, ya kuma kunshi kwamishinonin da suke kula da bangaren jinkai da tallafa wa al’umma na jihohin Borno, Adamawa da jihar Yola; shugabanin SEMA, NEDC da NCFRMI; hadi da wakilan soji, hukumar tarayyar Turai, hukumar raya kasashen duniya da kuma ofishin kasar Amurka kan kula da aiyukan jinkai.

Kwamitin ya sha alwashin gudanar da aiyukan da aka daura masa domin tabbatar da bada goyon baya da agajin kwarewa kan yadda za a tafiyar da aiyukan da suka shafi agaji da jinkai ga al’umman Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply